1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Olaf Scholz na ziyara a Amirka

Binta Aliyu Zurmi
February 7, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya isa birnin Washington na Amirka domin ganawa da shugaba Joe Biden a kan rikicin kasar Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/46eIc
USA Bundesfinanzminister Olaf Scholz in Washington DC
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Da ya ke jawabi ga manema labarai kafin ganawarsa da Shugaba Biden, Mr. Scholz ya ce tabbas Rasha za ta dandana kudarta mudin ta shiga kasar Ukraine.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Amirka ke gargadin mamyar da Rasha ke yunkurin yi a gabashin Ukraine na iya faruwa a 'yan kwanakin nan ko makwannin da ke tafe.

Wannan ziyara ta Scholz  a Amirka don zantawa da Biden kan rikcin na Ukraine dai na zuwa ne daidai lokacin da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ke ziyara a Moscow don tattaunawa da takwaransa Vladmir Putin kan rikicin na Ukraine.