Shugaban Iran ya bude sabuwar tashar makamashin nukiliya a Arak
August 26, 2006Talla
Shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad ya sake jaddada ´yancin kasarsa na mallakar fasahar nukiliya. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake kaddamar da wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa a garin Arak. Wannan tashar ita zata samar da ruwan da ake bukata ga wata tashar binciken makamashin nukiliya da ke kusa wadda a halin yanzu ake aikin gininta. Ana kuma iya yin amfani da wannan ruwa da tashar zata samar wajen sarrafa ingantaccen sinadarin plutonium da za´a iya kera makamin nukiliya da shi. Hakan dai wani muhimmin mataki ne ga shirin nukiliyar gwamnatin Teheran wanda kasashen yamma ke zargi shirin kera makaman nukiliya. To amma gwamnatin Iran ta dage cewar aikace aikacen ta na nukiliya don samar da makamashi ne ga farar hula. A ranar 31 ga watannan na agusta wa´adin da kwamitin sulhun MDD ya ba ta na ta dakatar da shirin sarrafa sinadarin uranium ya ke karewa.