1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Iran ya soki kasashen yamma

September 20, 2006
https://p.dw.com/p/Buiu

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinajad ya soki kasashen Amurka da Biritaniya, da cewa sune kashin bayan daya haifar Mdd take rasa kima da kuma daraja.

Ahmadinajad ya fadi hakan ne kuwa, a yayin da yake gabatar da jawabi a gaban babban zauren Mdd a jiya talata.

A lokacin bayanin Mahmud Ahmadinajad, ya kuma nanata aniyar kasar sa na ci gaba da sarrafa sanadarin Uranium don inganta rayuwar yan kasar.

Haka kuma, Shugaban na Iran ya kuma soki lamirin kasar Amurka na gabatar da yaki akan Iraqi a hannu daya kuma da Israela game da kakagidan da takewa yankin Palasinawa.

Kafin dai Jawabin na Ahmadinajad, Shugaba Bush a nasa jawabin ya bukaci Iran data yi watsi da aniyar ta na mallakar makamin na Atom.

Shugaba Bush yace, ba aniyar mu bane mu hana Iran mallakar fasahar ta nukiliya don zaman lafiya, kamar yadda take ikirari, to amma ana nan ana kokarin warware wannan rikici ta hanyar ruwan sanyi.

Rahotanni dai sun nunar da cewa batun rikicin nukiliyar kasar Iran na daga cikin manyan batutuwan da wannan taro na Mdd zai fi mayar da hankali akai, ba´a da bayan halin rashin zaman lafiya da ake fuskanta a yankin gabas ta tsakiya da kuma yankin Darfur na Sudan.