1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Iran yace zai kare mutuncin kasarsa

April 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0l

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmedinejad yace,shi fa ba gudu ba ja da baya a kokarinsa na kare martabar kasarsa.

A ci gaba da kalamansa akan kasar Israila kuma,Ahmedinejad yace,kasar ta yahudawa ba zata ci gaba da kasancewa ba,tunda a cewarsa kasa ce ta jabu,kuma kamata yayi wadannan bakin haure a yankin Palasdinu su koma inda suka fito.

Yace kasashen turai sune suka tilasatawa yahudawa komawa yankin na Palasdinu saboda kyamar yahudawan da suke yi.

Game da batun Iraqi kuma,shugaban na Iran cewa yayi,babu wata bukatar tattaunawa da Amurka game da wannan batu,tunda yanzu an samu kafuwar gwamnati a Iraqi.

Game da shirinsa na nukiliya kuma,yace yana ganin ba zaa lakabawa kasarsa takunkumi ba kuma kamata yayi a bar kasar ta Iran ta gudanar da aiyukanta yadda take so,yace bai kamata komitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya yarda wasu kasashe suna tilasta masa ba,ya kamata yayi aiki bisa dokokin kasa da kasa.