1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Iran yace,tayin kasashen turai wani mataki ne ga batun nukiliyarta

June 16, 2006
https://p.dw.com/p/Butq

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmedinajad yace,tayin da akayiwa kasarsa wani mataki ne mai muhimmanci da yace zasu duba shi sannu a hankali.

Bayan tataunawarsu a yau da shugaban kasar Sin,Ahmedinajad ya fadawa manema labari cewa,zai mayarda martani a lokacinda ya dace,ya kuma kara jaddada cewa,shirinsa na nukiliya na lumana ne.

Shugaban na Iran yace kasar Amurka itace kasa kadai a duniya data taba jefa bam din kare dangi akan kasar Japan a lokacin yakin duniya na biyu.

Yace kuma bai kamata ayi anfani da barazanar kafa takunkumi domin matsawa kowace kasa ba.

Ahmedinajad ya kuma baiyana cewa,kasar Iran tana da karfin kare kanta daga kowane irin barazana.

Da yake magana game da batun kisan gilla na yahudawa,shugaban na Iran yace,babu banbanci tsakanin yahudawa musulmi ko kirista,idan an tabo batun mutunci ko yancin dan adam a ko ina cikin duniya.