Shugabancin CDU zai yi murabus
October 7, 2021Talla
Armin Laschet ya gayawa manema labaru cewa za su gaggauta magance matsalar CDU ta hanyar jagorancin jam'iyyar zuwa kwamitin zartarwa na tarayya, ya kara da cewa zai gabatar da ranar da za a gudanar da babban taron jam'iyyar don warware wadannan batutuwa.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka dage cigaba da tattaunawar kulla kawance zuwa makon gobe inda ake fatan cimma dai-daiton kafa gwamnati.