1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaban Jamus na son a yi nazari kan rigakafin corona

January 12, 2022

Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya yi kiran da a yi zaman muhawara a game da shirin tilasta wa mutane a game da yin rikagafin corona a Jamus.

https://p.dw.com/p/45Qil
Steinmeier Diskussionsrunde mit Bürgern und Bürgerinnen zur Impfpflicht
Hoto: Chris Emil Janßen/imago images

Shugaba Steinmeier, ya ce akwai bukatar samar da gamsassun hujjojin daukar wannan mataki na sanya rigakafin tilas a kan Jamusawa kafin a kai ga yin hakan. A nashi bangaren shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya goyi bayan wajabta rigakafin a kasar.

Gaba kadan cikin wannan wata na Janairu ne dai 'yan majalisar dokoki za su yi zama domin tabbatar da kudurin da aka gabatar musu game da batun. Cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa a Jamus ta fitar da alkaluman mutum dubu 80,430 a rana guda, adadin kuma da ba a ga irin sa ba tun lokacin da corona ta bulla a duniya.