1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus ya yi wa Gambiya alkawura

Mouhamadou Awal Balarabe
December 14, 2017

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce kasarsa zata taimaka wa Gambiya magance matsalar tsaro da kuma zaman kashe wando da matasa ke fama da shi.

https://p.dw.com/p/2pLSG
Ghana - Bundespräsident Steinmeier
Hoto: picture-alliance/dpa/B. v. Jutrczenka

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier na ci gaba da rangadin wasu kasashen Afirka, inda baya ga Ghana ya ya da zango a kasar Gambiya. Steinmeier ya yaba canjin gwamnati da aka samu daga Yahya Jammeh wanda ya shafe shekaru 22 a kan mulki zuwa ga Adama Barrow a wannan kasa ta yammacin Afirka a farkon wannan shekarar.

Yayin wata kasaitacciyar liyafa da aka shirya masa a birnin Banjul, shugaban na Jamus ya ce kasarsa zata taimaka wajen inganta tsaro, da habaka al'adu tare da samar da ayyuka ga 'yan zaman kashen wando a Gambiya, inda ya ce samun hanyar dogaro da kai ne kawai zai sa matasa daina yin hijira ba bisa ka'ida ba da nufin zuwa Turai.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa mutane fiye da dubu 150 sun shiga Turai ta barauniyar hanya a  wannan shekarar da muke ciki.