Ziyarar Hassane Rouhani a Faransa
January 28, 2016Dukkanin shugabanin biyu dai zasu tattauna ne akan irin rawar da zasu taka ne a musamman a kasashen Syriya da Yemen gami sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi a tsakanin su.
Kazalika Shugaba Hassane Rouhani da Francois Hollande za kuma su rattaba hanu akan wasu yarjeniyo 20 domin kara habaka harkokin kasuwanci da huddar diplomasiya a tsakanin su.
Ayayin jawabin sa a gaban kungiyar 'yan kasauwar Faransa Hassane Rouhani yace :Mun hallara ne a nan domin tattauna batun harkokin kasuwanci gami da kara karfafa dangantaka ta Faransa tare da yin aiki da Faransan kan makamashi hade da jajircewa da a bangaren siyasar Iraniyawa a yau.
Kazalika Francois Hollade ya jinjinawa kasar Iran abisa yarjeniyoyin da suka rattabawa hannu gami yunkurin ta na sake bude wani sabon babi da kasashen duniya.