1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Iran na ziyara a Italiya

Salissou BoukariJanuary 25, 2016

Shugaba Hassan Rohani na Iran ya soma wata ziyara a Italiya wadda ke zama ziyararsa ta farko a wata kasar Turai, domin tattauna huldodi na kasuwanci.

https://p.dw.com/p/1HjXb
Hoto: Reuters/T. Gentile

Wannan ziyara dai ta ta'allaka ne kan batun huldar kasuwanci, a daidai lokacin da akasarin kanfanoni ke neman sake buda kofofinsu ko kuma zuwa kasar ta Iran bayan dage mata takunkumi. Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella ne ya karbi shugaban na Iran inda za su ci abincin rana tare, sannan da yamma shugaba Rohani zai yi abincin dare da shugaban gwamnatin ta Italiya Matteo Renzi.

A ranar Talata ne da safe aka tsara shugaban na Iran zai gana da Fafaroma Fransis shugaban darikar Katolika na duniya. Tuni dai hukumomin na Italiya suka amince da kaucewa amfani da giya ko wani abun mai sa wa maye cikin dukkannin abincin da tawagar da kasar Iran za bukata.