Ziyarar shugaban Jamus na farko a Masar cikin shekaru 20
September 10, 2024Baya ga batun inganta huldar kasuwanci tsakanin kasashen Masar da Jamus, a halin yanzu, gwamnatin Jamus ta zuba jari a kamfanoni 1,620 da ke aiki a duk sassan tattalin arzikin Masar. Wadannan kamfanoni suna ba da gudummawa ga sauya cibiyoyin fasaha zuwa tattalin arzikin Masar tare da samar wa dubban mutane ayyukan yi a fadin kasar.
Shugaba Steinmeier da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi za su tattauna hanyar warware rikin Isra'ila da Gaza da ya jefa yankin Gabas ta tsakiya cikin rashin zaman lafiya. Dama dai Masa da Katar na kan gaba cikin kasashen da ke yunkurin shiga tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas don samar da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Zijyarar Steinmeier na zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan fafutuka ke zargin gwamnatin Al-Sisi da takun siyasa irin na mulkin kama karya, Shuagban na Jamus Frank-Walter Steinmeier, zai kuma gana da kungiyoyin kare hakkin 'yan Adam da cibiyoyin siyasar kasar Jamus da ke Masar.