1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Kenya mayar da dokar haraji ga majalisa

Suleiman Babayo
June 26, 2024

Shugaban kasar Kenya ya yi watsi da dokar da ta haifar da zanga-zanga a kasar inda ya mayar da dokar zuwa majalisar dokoki domin gyare-gyare bayan zanga-zangar da ta halaka mutane 23 sannan wasu 30 suka jikata.

https://p.dw.com/p/4hXJ1
Kenya | Jami'an tsaron lokacin zanga-zanga a Kenya
Jami'an tsaron lokacin zanga-zanga a KenyaHoto: Brian Inganga/AP Photo/picture alliance

Shugaba William Ruto na Kenya ya yi watsi da dokar fadada haraji da majalisar dokoki ta amince da ita, abin da ya haifar da zanga-zanga a kasar, inda ya sake mayar da dokar majalisar domin gyare-gyare. Majalisdar tana zama na musamman karkashin tsauraran matakan tsaro, inda majalisar ta amince da tura sojoji kare gine-gine masu muhimmanci lokacin zanga-zanga.

Karin Bayani: Matasa a Kenya sun kona majalisar dokokin kasar

Kenya | Jami'an tsaron lokacin zanga-zanga a Kenya
Jami'an tsaron lokacin zanga-zanga a KenyaHoto: LUIS TATO/AFP

Tun farko Kungiyar likitoci ta kasar ta tabbatar da mutuwar fiye da mutane 20 kana wasu kimanin 30 suka jikata sakamakon zanga-zangar da aka fuskanta a fadin kasar a wannan Talata da ta gabata, domin kiyayya bisa sabuwar dokar da majalisar dokokin kasar ta amince ta fadada haraji kan kayayyaki a kasar.

Wannan na zuwa lokacin da masu zanga-zangar ke cewa za su sake komawa kan tituna a gobe Alhamis, domin nuna mutuntuwa ga masu zanga-zangar da suka mutu lokacin artabu da jami'an tsaro, kamar yadda masu shirya zanga-zangar suka nunar a shafukan sada zumunta musamman na X ko kuma Twitter. Ana sa bangaren Shugaba Ruto na kasar ta Kenya ya yi zargin cewa masu tayar da zaune tsaye sun karbe ragamar zanga-zangar.