1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya na fuskantar barazana

March 22, 2017

Jagoran majalisar dattawan Najeriya na fuskantar wani sabon zargi na kin biyan harajin Kwastan na wata motar miliyoyin Nairori.

https://p.dw.com/p/2ZhIf
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Majalisar dattawan Najeriya, za ta binciki shugabanta Sanata Bukola Saraki da ake zargi da kin biyan harajin kwastan na wata motar sulke da ya mallaka. Wannan binciken dai ka iya sa a tsige Sarakai daga mukami na uku mafi girma a kasar, dan kuma jami'iyyar gwamnati mai ci, muddin aka same shi da laifi.

Wani mai magana da yawun Sarakin Yusuph Olaniyonu, ya ce maganar wadda Sanata Ali Ndume ya gabatar a ranar Talata a zauren majalisar dattawa, babu gaskiya a ciki. Sanata Bukola Saraki wanda shi ma ya musanta zargin da ake masa, na fuskantar wani zargin mai nasaba da yin karya kan bayanan kadarorin da ya mallaka, lokacin da ya rike mukamin gwamnan jihar Kwara a baya.  Motar Sarakin dai ta kai darajar Naira miliyan 298.