Shugaban Najeriya ya nuna ɓacin rai game da hare-haren Kano
January 22, 2012Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da sanarwa game da munanan hare-haren kano, a inda ta yi Allah wadai tare da bayyana su da aikin maƙiya mulkin demokaraɗiya. Wannan martanin ya zo ne sa'o'i da dama bayan hare-haren da ƙungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kaiwa
A halin yanzu dai mutane aƙalla 160 ne aka tabbatar cewa sun rasa rayukansu a sakamakon tashin bama bama da aka samu a birnin kano. Sama da bama bamai 20 suka tashi a birnin da ke arewacin tarayyar ta Najeriya a ranar jumaa da ta wucce a wurare daban daban ciki kuwa har da hekwatar rundunar 'yan sanda ta jihar.
Yanzu haka dai jama'a na cikin zaman fargaba a kanon inda hukumomi suka kafa dokar hanna fita na sa'o'i 24.Kungiyar Boko Haram ta riga ta ɗauki alhakin waɗannan tagwayen hare-hare.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu