1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya ya nuna ɓacin rai game da hare-haren Kano

January 22, 2012

Gwamnatin Najeriya ta yi tofin Allah tsine ga munanan haren da suka salwantar da rayukan mutane aƙalla 160 a Kano. Sai dai al'umar wannan jiha da ke arewacin kasar na zaman fargaba.

https://p.dw.com/p/13nsf
epa03046191 (FILE) A file photograph Goodluck Ebele Jonathan, President and Commander-in-Chief of the Armed Forces of the Federal Republic of Nigeria speaks during the general debate at the 66th session of the United Nations General Assembly at United Nations headquarters in New York, New York, USA, on 21 September 2011. Media reports state on 31 December 2011 that President Goodluck Jonathan has declared a state of emergency in areas affected by attacks from the Islamist group Boko Haram. Borders will be temporarily closed in the north-eastern states of Yobe and Borno, and central state of Plateau. EPA/JASON SZENES *** Local Caption *** 00000402928322 +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaban Goodluck Jonathan na NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da sanarwa game da munanan hare-haren kano, a inda ta yi Allah wadai tare da bayyana su da aikin maƙiya mulkin demokaraɗiya. Wannan martanin ya zo ne sa'o'i da dama bayan hare-haren da ƙungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kaiwa

A halin yanzu dai mutane aƙalla 160 ne aka tabbatar cewa sun rasa rayukansu a sakamakon tashin bama bama da aka samu a birnin kano. Sama da bama bamai 20 suka tashi a birnin da ke arewacin tarayyar ta Najeriya a ranar jumaa da ta wucce a wurare daban daban ciki kuwa har da hekwatar rundunar 'yan sanda ta jihar.

Yanzu haka dai jama'a na cikin zaman fargaba a kanon inda hukumomi suka kafa dokar hanna fita na sa'o'i 24.Kungiyar Boko Haram ta riga ta ɗauki alhakin waɗannan tagwayen hare-hare.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu