Shugaban Nijar na neman shawo kan matsalar lantarki
April 8, 2013
Hukumar kididdiga ta Jamhuriyar Nijar ta nunar da cewa a shekara ta 2012 kasar ta yi amfani da wutar lantarki da ya kai yawan Megawatts 550. Wannan na nufin cewa kashi 8% na fadin kasar ne ke cin gajiyar wannan makamashi a garuruwa kimanin 300 na kasar. A halin yanzu ma dai akwai makeken gibi tsakanin kauyuka da kauyuka; inda kashi 44% na mazauna birane ke samun lantarki yayin da kasa da 2,5% na yankunan karkara ke amfani da wutar lantarki. Kashi 64% na wutar lantakin da ake sha a Jamhuriyar Nijar na fitowa ne daga makobciyarta Tarayyar Najeriya.
Sai dai akasarin garuruwan da su ke amfani da lantarkin a Nijar na fama da tsikewarta a a lokutta da dama musammana lokutan zafi wato kaka. Masana'antu ciki kuwa har da na birnin Yamai na amfani da janareto bayan katsewar wutar lantarki domin samun makamashin da suke bukata. Wannan matsala na kawo cikas a harakokin yau da kullan na al'uma da ma masana'antu. Saboda haka ne suke yawaita yin korafi game da wannan matsala.
Matakan cike gibin wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar
A 'yan shekaru nan gwamnatin kasar Nijar ta dukufa wajen samar da hanyoyin shawo kan wanann matsala ta karancin wutar lantarki. A makon da ya gabata(04.04.2013) gwamnati ta gudanar da bikin dora tubalin farko na gina wata sabuwar cibiyar lantarki da za ta samar da karin Megawatts 100. Ministan makamashi da fetur na Nijar Fumakoy Gado ya ce matakai da dama gwamnatinsu ta dauka domin magance karancin wutar lantarki a Jamhuiriyar Nijar.Fadar mulki ta Yamai ta kuma dukufa wajen samar da makamashin lantarki ta hanyar hasken rana a inda tuni kanfanin man fetur da kasar ta mallaka ya lamshe kashi 10% na makamashin da kasar ke amfani da shi.
Rahotanni cikin sauti na kasa
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe