Shugaban Pakistan ya sanarda tube kakinsa na soja
November 26, 2007Shugaban ƙasar Pakistan Parvez Musharraf ya sanarda cewa zai sauka daga mukamin babban hafsan sojojin ƙasar kuma a rantsar da shi a matsayin shugaban gwamnatin farar hula a ranar alhamis.Wannan shine karo na farko da Musharraf ya yanke ranar da zai sauka daga babban hafsan tare da maido da gwamnatin farar hula a kasar.A halinda ake ciki kuma tsofin firaministoci wato Benazir Bhutto da Nawaz Sharif sun cike takardunsu na tsayawa takara a zaben ranar 8 ga watan disamba kodayke dukkaninsu biyu sun yi barazanar janyewa daga zaɓen.A ranar lahadi Nawaz Sharif ya koma gida daga gudun hijira a kasar Saudiya.Ya ce ba zai amince da shugabancin Musharraf ba koda kuwa ƙarkashin gwamnatin farar hula.Sai kuma babu tabbacin ko gwamnati zata amincewa Nawaz Shariff shiga wannan zabe.