An bayyana sakamakon zaben Saliyo
June 27, 2023Hukumar zaben Saliyo ta bayyana Shugaba Julius Maada Bio, na jam'iyyar SLPP mai shekaru 59 a matsayin wanda ya lashen zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Shugaba Bio ya samu kashi 56 cikin 100 na kuri'un da aka kada abin da ya tabbatar da cewa ya kaucewa tafiya zagaye na biyu na zabe da jagoran 'yan adawa Samura Kamara mai shekaru 72 da haihuwa na jam'iyyar APC wanda yake matsayi na biyu da kashi 41 cikin 100 na kuri'un.
Tun farko babbar jam'iyyar adawa ta kasar APC ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar na wucin gadi, inda 'yan adawa suka yi zargin tafka magudi. Ana zaman tankiya tun bayan zaben da Shugaba Bio ya fafata da sauran 'yan takara 12.
Ita dai kasar Saliyo da ke yankin yammacin Afirka a baya ta yi fama da matsalolin annobar cutar Ebola a shekara ta 2014 sannan ta fuskanci yakin basasa tsakanin 1991 zuwa shekara ta 2002 inda fiye da mutane 50,000 suka halaka.