Shugaban Togo na da tabbacin yin tazarce
April 23, 2015Madugun 'yan adawan Kasar Jean-Pierre Fabre ya fi mayar da hankalisa a karkarar Togo wajen tallata kansa.Yayin da shugaba mai barin gado ya yi amfani da hanyoyin sadarwa na zamani tare da shiga sassan kasar wajen jan hankali masu kada kari'a.
Su dai 'yan adawan kasar ta Togo sun kasa fitar da dan takara daya tilo da zai kalubalanci shugaba mai barin gado Faure Gnassinbe a zaben da zai gudana a ranar Asabar mai zuwa. Saboda haka ne ake ganin cewar ko makamawa babu zai samu yin tazarce bayan wa'adin mulki biyu.
'Yan Togo da dama sun zargi shugaban Faure Gnassingbe da gaza inganta halin rayuwar 'yan kasar wadanda galibinsu ke rayuwa da kasa da Dolla daya na Amirka a kowace rana. Shugaban ya gaji mahaifinsa ne Gnassingbe Eyadema wanda ya rasu bayan da ya shafe shekaru 38 ya na mulki.