1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Gnassingbe zai tsawaita wa'adin mulki

Abdul-raheem Hassan
May 7, 2024

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe, ya rattaba hannu kan wata sabuwar kundin tsarin mulki mai cike da cece-kuce wanda ya kawar da zaben shugaban kasa kai tsaye, tare da ba wa 'yan majalisa damar zaban shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/4fano
Shugaban kasar Togo, Faure GnassingbeHoto: Zuma/IMAGO

Dokar, na nufin daga yanzu majalisar dokoki ce ke da ikon zaban shugaban kasa, maimakon zaben kai tsaye da aka saba. Kazalika sabon kundin tsarin mulkin ya kuma kara wa'adin shugaban kasa daga biyar zuwa shekaru shida a gefe guda tsawon mulkin Shugaba Gnassingbe na kusan shekaru 20 baya cikin lissafi.

Sai dai tuni 'yan adawa ke danganta matakin shugaban da yunkurin tsawaita mulkin mahadi ka ture da iyalin gidan ke yi tsawon shekaru.