1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Togo ya tsaya takara a karo na hudu

Mouhamadou Awal Balarabe
January 9, 2020

Faure Gnassingbé na daga cikin wadanda suka mika takardun takararsu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta Togo. Zai kalubalnci 'yan takara tara a zaben shugaban kasa na 22 ga wata mai zuwa.

https://p.dw.com/p/3VwQU
Faure Gnassingbe bei der Abgabe seines Stimmzettels zur Parlamentswahl in Togo am 25.07.2013
Hoto: Reuters/Noel Kokou Tadegnon

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Togo ta bayyana cewa mutane 10 sun ajiye takardun takara a zaben shugaban kasar da zai gudana a ranar 22 ga watan Fabrairu mai zuwa.  A lokacin da yayi bayani ga manaima labarai a birnin Lome, shugaban CENI na kasa Tchambakou Ayassor ya ce kotun tsarin mulki ce za ta tantacen sunayen wadannda za su fafata tsakaninsu. Madugun 'yan adawan Togo Jean-Pierre Fabre da kuma Shugaba da ke ci yanzu Faure Gnassingbé da ke neman wa’adi na hudu na daga cikin 'yan takara. 


 Kasar Togo ta yi fama da rikicin siyasa tsakanin 2017 zuwa 2018 sakamakon bukatar 'yan adawa ta neman takaita wa’adin shugabanci da neman Faure Gnassingbé ya sauka daga mulki. Sai dai 'yan majalisa sun sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa Shugaba Gnassingbé damar sake tsayawa a zaben a cikin 2020 da 2025, tare da samar da rigar kariya ta tsawon rayuwa dangane da laifuffukan da ya aika a lokacin da yake mulki.