Turkiyya: Erdogan ya nada sabbin ministoci
June 4, 2023Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fitar da sunayen ministocinsa 'yan sa'o'i bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a wa'adi na uku. Ya sanar da wani kwararren mai leken asiri a matsayin ministan kula da harkokin wajen kasar. Tsofaffin ministocinsa guda biyu da suka hada da mai kula da ma'aikatar lafiya da al'adu ne kawai shugaban na Turkiyya ya sake bai wa sabon mukami a sabuwar majalisar zartaswar da ya kafa.
Rantsar da shi da aka yi a ranar Asabar a gaban shugabannin duniya fiye da 20 da suka halarci bikin a birnin Ankara, ya biyo bayan nasarar da Erdogan din ya samu a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon da ya gabata.
Erdogan dai shi ne shugaban da ya fi dadewa yana mulki a tarihin siyasar Turkiyya. Tun daga shekara ta 2003, lokacin da ya hau karagar mulki, gwamnatinsa ta sha fuskantar kalubalen zanga-zanga da zarge-zargen cin hanci har ma da yunkurin juyin mulki, amma kuma yana tsallakewa. Sai dai a yanzu yana fuskantar babban kalubalen tsadar rayuwa da ke ci gaba da addabar kasashen duniya.