Erdogan ya yi barazanar daukar fansa kan gwamnatin Siriya
February 12, 2020Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wannan Laraba ya ce kasarsa za ta kai hari kan dakarun gwamnatin kasar Siriya a ko-ina cikin Siriyar matukar an sake ji wa wani sojin Turkiyyar rauni.
Erdogan ya fada wa wani taron jam'iyyarsa a birnin Ankara cewa Turkiyya ta kuduri aniyar mayar da hannun agogo baya na nasarorin da sojojin Siriya suka samu a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar.
Ya ce: "Daga yau matukar an yi wa sojojinmu rauni kuma komin kankantarsa, za mu kai farmaki kan sojojin gwamnati a ciki da wajen iyakokin lardin Idlib, ba tare da la'akari da yarjejeniyar Sochi ba."
Karkashin yarjejeniyar Sochi da aka cimma tsakanin Rasha da Turkiyya a shekarar 2018, Turkiyya ta kafa sansanonin sanya ido guda 12 a Idlib, inda kuma take mara wa wasu kungiyoyin 'yan tawaye baya.
Akalla sojojin Turkyya 13 aka kashe a wani harin bindigogin atileri na Siriya a wannan wata.