Shugaban Ukraine Yanukovic na tsaka mai wuya
May 1, 2012Bisa rade-radin cewa manyan shugabanin Turai zasu kauracewa gasar cin kofin kwallon kafar Nahiyar ta shekarar 2012, wanda ake sa ran gudanarwa a watan Yuni a kasashen Ukraine da Poland, gwamnatin Ukraine ta yi gargadin cewa yin hakan mataki ne mai kama da yakin cacar baka da aka gudanar a shekarun baya, kuma ba zai haifar da da mai ido ga lamuran da suka shafi zamantakewar Turai ba.
Oleg Woloschin mai magana da yawun hukumar kula da harkokin wajen Ukraine, ya ce yana fata jita-jitar da ake yadawa, na cewa manyan 'yan siyasar Jamus zasu kauracewa gasar cin kofin kwallon kafar ta shekarar 2012 ba gaskiya bane, kuma labari ce kawai ta 'yan jarida, domin a cewarsa kauracewa gasar a matsayin wani mataki na siyasa da kuma nuna adawa da yadda kasarsa ke tafiyar da al'amuran da suka shafi madugun adawar kasar wato Juliya Tymoshenko tamkar komawa zamanin yakin cacar baka ne.
Barazanar zama saniyar ware
'Yan siyasan Jamus na kokarin mayar da gasar wani abun siyasa ne kawai a wani sukan da fadar gwamnatin Ukraine da ke Kiev ta yi wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Bisa bayyanan 'yan jamiyyar Yanukovic, tayin gwamnatin Jamus na kawo Tymoshenko kasarta domin bata magunguna babban katsalandan ne a cikin harkokin da suka shafi Ukraine. A cewar su Merkel ta mance cewa kasar Jamus ta ke shugabanta ba Ukraine ba.
Ga Wadim Karasjow wani masanin siyasa da ke birnin Kiev, shugaban kasar Ukraine Yanukovic ya shiga duhu domin a tunaninsa yafewa Tymoshenko ba zai taimake shi ba, kuma tsare ta da yake cigaba da yi, na jefa shi a wani mawuyacin hali.
"Yanukovic na fargabar cewa zata sami karbuwa daga wurin dukka shugabanin nahiyar Turai. Kasancewarta a gidan kaso na hana hakan daga faruwa, duk da cewa tsaretan na cigaba da jan hankula, amma idan ya sake ta, goben nan zata gana da Merkel da Sarkozy ko kuma ma da Van Rompoy, shugaban zartarwar Tarayyar Turai. Ita 'yar siyasa ce a matakin kasa da kasa watakila ma ta gana da Obama da Putin wannan kuma a bayyane ya ke cewa Janukowich zai sami kansa a matsayin saniyar ware"
Matsin kaimi daga kasashen Turai
Haka dai kasashen Turan ke cigaba da matasawa gwamnatin Yanukovic lamba. Shugabanin kasashen Austriya, Slovenia da jamhoriyar check duk sun soke ziyarar da suka yi niyyar kaiwa Ukraine.
A cewar shugaban kasar jamhoriyar Check Vaclav Klaus babban dalilinsa shine cin zarafin tsohuwar Frime minista Tymoshenkon da gwamnati ke yi. Shugaban kasar Rasha Dimitri Medvedev ya nunar da cewa matakin gwamnatin kasar a kan Tymoshenko bai dace ba.
A harkokin siyasa mutun na da damar gwawarmaya kwatar kansa da duk karfin da yake da shi, to amma an danne wannan dama idan har aka jefa mutun a kurkuku. Dangane da tambayar ko shin Yanukovic ya damu da sukan da kasashen ketare ke yi masa?, Karasjow, masanin siyasan nan da ke birnin Kiev ya yi bayani
"A takaice yana tsoron sukan da yake sha daga kasashen waje amma ya fi jin tsoron Tymoshenko sai dai a zahiri ya fi fargabar rasa iko. bashi da wata fargabar cewa za'a kauracewa gasar kwallon kafar ta shekarar 2012 a dalilin Tymoshenko. A bayyane ya ke cewa gwamnati ba zata iya bari a soke gasar ba, dan haka za'a gudanar da ita."
Abun da ya fi mahimmanci ga Yanukovic yanzu shine jamiyyarsa ta fito mafi karfi a zaben majalisar dokokin da za'a gudanar a watan Oktoba idan Allah ya kaimu. Bisa ra'ayin masu sanya ido babu yadda za'ayi abokiyar hammayar ta sa, wato Tymoshenko ta sami damar taka rawar gani.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Saleh Umar Saleh