Shugaban ƙasar Iran na tattaunawa da takwaransa na Masar
February 5, 2013Shugaban wanda ya isa a birin Alƙahira domin halatar taron ƙungiyar ƙasashen musulumi ta OCI, shi ne wani shugaba na farko na Iran da ya kai ziyara a Masar tun a shekara ta 1979 lokacin da a ka yi juyin juya hali na ƙasar.
Gidan telbijan na Masar ya nuno Mahmoud Ahmadinejad tare da takwaransa Mohamed Mursi suna yin gaisuwa a lokacin da ya ke tarbon shi, abin da a wani lokaci a ƙasar zamanin mulkin Hosni Moubarak ba'a taɓa tsammanin haka ba zata faru. Ga tsohon shugaban da ke baiwa ƙasashen yammancin duniya goyon baya dangane da maganar yankin gabas ta tsakiya. Shugabannin biyu sun tattauna rikicin Siriya da kuma batun sake ƙulla hulɗa da ta tsinke tsakanin su tun a shekara ta 1980.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman