Shugabanni a Kataloniya za su kai kara MDD
February 1, 2018Talla
Shugabanni uku daga yankin Kataloniya da aka dauresu a Spain sakamakon shigarsu dambaruwar siyasar yankin a kokarin ballewa daga kasar Spain sun bayyana cewa za su kai kukansu ga 'yan fafutika na Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda lauyansu a birnin London ya bayyana a wannan rana ta Alhamis.
A cewar lauyansu Ben Emmerson tsarewar da mahukuntan kasar Spain suka yi masu an tsarata ne don hana masu dama ta shiga harkokin siyasa a matsayinsu na wakilan al'ummar yankin Kataloniya. Lauya Emmerson ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a wannan rana.