1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin APC na ganawa da bangaren PDP

Usman ShehuOctober 31, 2013

Shugabannin APC na ziyartar gwamnonin PDP da su ke adawa da uwar jam'iyar, domin zawarcin gwamnonin su shigo APC

https://p.dw.com/p/1A9sc
Gen. Muhammadu Buhari, presidential candidate of the Congress for Progressive Change, attends a campaign rally in Lagos, Nigeria, Wednesday, April 6, 2011. Buhari, a former military ruler of Nigeria, has gained support in his third bid to become president of the oil-rich nation. Buhari ruled Nigeria from 1983 to 1985 after a military coup deposed the elected president. (AP Photo/Sunday Alamba)
Hoto: AP

Yayin da zaman doya da manja ke kara tsami, tsakanin gwamnonin nan bakwai da bangaren shugabancin jamiyyar PDP na kasa karkashin Alhaji Bamanga Tukur, yanzu haka alamomi sun fara karkata cewar, wasu da ga cikin gwamnonin za su tattara yanasu-yanasu, domin sauya sheka zuwa babbar jamiyyar hamayya ta APC. Alamar hakan shi ne a yau Alhamis, manyan jagororin jamiyyar ta APC karkashin jagorancin janar Muhammadu Buhari mai ritaya, suka mika goron gayyata kai tsaye ga gwamnan jihar Kano Eng. Rabiu Musa Kwankwaso. Inda suke godon ya dawo sabuwar tafiya karkashin APC, a wani gagarumin biki da aka gabatar a fadar gwamnatin jihar Kano.

Rabiu Musa Kwankwaso, Gouverneur von Kano. Thomas Mösch, 9.5.2013, Kano/Nigeria. Rabiu Musa Kwankwaso, Gouverneur von Kano State (Nigeria) seit 2011 (bis 2015) und zuvor von 1999 bis 2003.
Rabiu Musa KwankwasoHoto: DW/T. Mösch

Wannan Goron gayyata dai ya kara nunawa duniya matsayin gwamna Kwankwaso, da tun asali aka jiyo shi yana barazanar cewar idan hagun ta kiya babu abinda zai hana komawa dama. An dai tarbi wannan tawaga a fadar gwamnatin jihar Kano da ake wa lakabi da Afrika House, cikin wani gagarumin biki da ke nuni da cewar, mai neman kashi ne aka jefe shi da kashin awaki. Tun da farko dai shugaban jamiyyar ta APC Chief Bisi Akande, ya bayyana dalilan da ya sanya su kawo wa gwamnan wannan goron gayyata.

Yace "Mun yanke wannan hukunci ne na kawo maka goron gayyata, domin sanin irin gallazawa da kuke fuskanta cikin jamiyyar ku, muna alfaharin tallata maka matsuguni cikin jamiyyar APC. Domin gurbi ne da ya dace da mutane irin ka, muna alfaharin shaida maka cewar, akwai kyakkyawan yanayi cikin ta domin mike kafa.

A nasa bangaren tsohon dan takarar shugabancin kasar yayin zaben 2011 janar Muhammad Buhari, ya fara ne da kokawa da halin rashin tabbas da kasar ke ciki, laifin daya dorawa jam'iyyar PDP mai mulkin kasar. Buhari ya kara da cewar wannan dalili ya sanya iyayen APC yanke shawarar zawarcin kwankwaso, sakamakon bukatar da wannan tafiya ke da shi ga mutane irinsa.

Da yake mayar da amsa gwamnan jihar kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jin dadi da wannan ziyara da kuma gamsuwa da ganin jiga jigan jamiyyar har fadar mulkin sa, ya basu kwarin gwiwar nazari kan wannan bukata da suka zo masa da ita, kafin yanke hukunci.

Jigawa State Governor Sule Lamido, speaks on September 27, 2010 in Dutse about the flood disaster in Nigeria's north. Officials in Jigawa state say two dams opened last month caused flooding that displaced some two million people. They have heavily criticised the agency in charge of the barriers, alleging similar episodes have occurred in the past. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Sule LamidoHoto: Getty Images

Sai dai a nasu bangaren magoya bayan jam'iyyar PDP tsohuwa dake biyayya ga shugabancin Alhaji Bamanga Tukur sun ce dama can kwankwason ba dan jam'iyyar su bane. Don haka ya kara gaba zai fiye musu masalaha, inji Shehu Wada Sagagi mataimakin kantoman jamiyyar a jihar Kano.

Wannan ziyara dai ta bude sabon babi a fagen siyasar jihar Kano da gwamnatin kwankwasiyya ke mulki, wannan ya sanya wasu ke hasashen cewar dama can an gama kullawa illa a bayyana komai

Tawagar da ta kawo wannan goron zawarci dai ta hada da tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Ahmed Tinubu, da gwamnonin jihohin Lagos da Imo da kuma Ekiti, sai kuma tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Modu Sharif da sauran iyayen jamiyyar. Tawagar kuma daga Kano ta zarce zuwa jihar jigawa, domin yin irin wannan zama da gwamnan jihar Sule Lamido.

Mawallafi: Nasir Salisu Zango

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani