Shugabannin duniya na jinjina ga Merkel yayin da mulkinta ke zuwa karshe
Bayan shekaru 16, nan ba da jimawa ba shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta fice daga fagen siyasa. Shugabannin duniya masu ci da wadanda suka sauka na ta yaba irin rawar da ta taka tsawon mulkinta.
Tsohon shugaban Amirka Barack Obama: 'Karshen godiya'
A sakon bidiyo zuwa ga shugabar gwamnatin a taronta na EU na karshe, Obama ya ce: "Kina bin masoyanki da sauran mutanen duniya baki daya bashin kyakkyawan matsayi tsawon shekaru da dama." Obama Ya yaba wa Merkel bisa yadda take sanya bukatunta a gaba da komai. Kila dai yana kwatanta yadda ta yi tsayin daka ne a 2015 game da matsalar 'yan gudun hijra.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa: 'Shekaru 16 na himmatuwa' kan Turai
A wani sako da ya fidda, Macron ya yaba da irin jajircewar Merkel a duk lokacin da Turai ta shiga babbar matsala, ciki har da annobar corona. "Godiya gare ki ya ke Angela da gwagwarmayar jagorantar Turai. Shafin Twitter ba zai cika takaitacce a shekaru 16 ba."
Shugaban Amirka Joe Biden: Babban 'aboki'
Dangantakar Joe Biden da Merkel mai karfin gaske ce. Biden na kiranta "babbar kawa kuma abokiyar Amirka" kuma yana yaba wa kwarin tsarin shugabancinta. Kawancen kasashen biyu ya yi tsami a mulkin wa'adi daya tak na Donald Trump, wanda ba kasafai suke hada ido ba.
Tsohon shugaban hukumar EU Jean-Claude Juncker: Ta 'gina Jamus a Turai'
Junker, dan siyasar Luxembourg, wanda ta yi aiki da shi shekaru da yawa ya bayyana inda suka yi sabani, amma ya fadi inda ra'ayinsu ya zo daya. "Tabbas ta gina Jamus a Turai. Ta fada wa Jamusawa cewar Turai wani bangaren Jamus ne, wato da Faransanci 'raison d'etat,' kuma wannan shi ne abin da ta bari a baya domin babu wani shugaban gwamnatin da zai zo bayan ta wanda ba mai ra'ayin Turai ba ne"
Shugaban majalisar zartarwar EU Charles Michel: 'Ke abar tarihi ce'
Shugabannin Turai na jinjina da yabon shugabar gwamnatin mai barin gado. Shugaban majalisar zartarwar EU Charles Michel, ya fada wa Merkel cewa "ke abar tarihi ce. EU ba tare da Merkel ba tamkar Rom ce ba fadar Vatican ko Faransa ba tare da Eiffel Tower" Dan Bulgeriyan ya ce shi da abokan aikinsa za su rasa shawari da basirar Merkel a lokacin da suke cikin kalubale na samar da tsarin Turai.
Firimiyan Birtaniya Boris Johnson: 'Gaskiyar Tarihi na sadaukarwa'
Goyon bayan Brexit ya zama ciwon kai a 'yan shekarun nan. Amma duk da haka a ziyarata ta watan Juli, Johnson ya fada wa Merkel cewa "kwarewar kimiyarki ya zama ginshikin koya wa duniya martanin da za su yi wa corona". Johnson ya kuma ya yaba wa basirar diflomasiyyarta. "Ina son in gode miki ba wai ga kawancen Birtaniya da Jamus ba, amma gaskiyar sadaukarwa ta tarihi na diflomisiyyar duniya."
Tsohon Firimiyan Birtaniya Tony Blair: '`Nasara ta ban mamaki'
Idan da Blair na da wata hanya da Birtaniya ba ta fice daga EU ba. Duk da kamarin Brexit, Merkel ta jagoranci magance matsalolin kungiyar da dama. Tsohon Firaministan ya yaba wa jajircewarta a shekarun nan inda ya ce "komai na kan hanya, nasara ce ta ban mamaki na iya rike Turai a dunkule a wannan lokaci mafi tsauri a jerin shekarun nan da Turai ta fuskanta"
Shugaban gwamnatin Ostiriya Alexander Schallenberg: 'Ita sararin samaniya ce wajen kwantar da hankali'
Sabon shugaban gwamnatin Ostiriya da aka nada bayan murabus din wanda ya gada Sebastian Kurz da aka tuhuma da cin hanci, ya san Merkel tun shekaru a matsayinsa na tsohon ministan harkokin waje; ya ce "za ta bar gurbi. Ita sararin samaniya ce wajen kwantar da hankali. Kuma ba dayan biyu ita babbar jigo ce a Turai"
Firimiyan Poland Mateusz Morawiecki: 'Ko yaushe ta na cikin sasanta lamaru'
Merkel ko da yaushe na ba da muhimmanci ga hulda tare da kasashe makwabtan gabashin Jamus, wanda akasari baya samuwa bisa bambancin ra'ayi, misali tsarin 'yan gudun hijira. Firaministan Poland Mateusz Morawiecki ya fadi hakan lokacin ziyarar ban kwanan da Merkel ta kai har ma ya ce "duk da yawan matsaloli mun ci gaba da kasancewa cikin tattaunawa, wanda bisa hakan nake gode miki"
Shugaban Recep Tayyip Erdogan: 'Abokiya' kuma 'shugaba mai mutunci'
Merkel ta samu matsaloli da yawa tare da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ba wai bisa kare hakkin jama'a kawai ba. Amma ya jinjina wa "abokiya" kuma "shugabar gwamnati mai mutunci" a matsayin kwararriyar 'yar siyasa wacce ko da yaushe ke da "basirar iya tinkarar lamari" kai Merkel sau da dama na neman yin magana da Erdogan, ba wai a kan shirin 'yan gudun hijira kawai ba.
Firimiyan China Xi Jinping: Merkel daddadiyar 'abokiyar China ce'
Merkel ko da yaushe tana cike da sha'awar habakar China; har sai kusan karshen wa'adinta ta fara yin shakka. Xi Jinping sakatare janar na jam'iyyar kwaminisanci kana shugaban kasa ya aiko mata sakon ban kwana ta bidiyo, inda ya kwatanta ta da "tsohuwar abokiyar China" Irin wannan girmamawa a fakaice, ita aka yi wa Vladimir Putin, Fidel Castro da Robert Mugabe.
Shugaba Putin na Rasha: Shekaru 16 masu kyau
Kimar Merkel wajen shugaban kasar Rasha Putin ba ta da karfi. "Tana kan mulki shekaru 16 abin tunawa ne' haka ya fada kwanan nan da aka tambaye shi ko zai yi keyawarta, ya ce tana ma iya yin takara kuma amsa ga dan siyasa mai mulki. Wannan hotonsu su biyu ne lokacin da Merkel ta kai masa ziyara a 2007, ya bar karensa mai suna Labrador ya sunsuni Merkel wacce aka san ta da tsoron kare.
Tsohon shugaban kasar Amirka George W. Bush: 'Mai aji da mutunci ce'
Merkel ta taba ziyartar Bush a wurin shakatawarsa da ke Texas kuma tsohon shugaban wanda akasari yanzu ke guje wa siyasa, ya himmatu ga yin zane kuma ya zana Merkel. Bush a kwannan nan ya fada wa DW cewa "Merkel ta kawo aji da mutunci a matsayi mai muhimmanci. Ta dauki tsauraran matakai kuma ta yi haka ne kan abin da ya fi alheri ga Jamus, hakan kuma ta yi ne a bisa ka'ida"