Shugabannin EU sun kasa yanke kudirori a taron kolinsu
July 17, 2014A karshen taron, shugabannin sun yanke shawarar sake haduwa tsakaninsu a karshen watan Agusta domin warware matsalolin da ke hana ruwa gudu a tsakaninsu.
Sabani mafi tsanani shi ne na tsakanin Italiya da wasu kasashe na gabashin Turai, a game da ko ya dace a mika mukamin kakakin harkokin waje na Kungiyar Hadin Kan Turai ga ministan harkokin wajen Italiya, Federica Mogherini. Firaministan Italiya dan jam'iyar gurguzu, Matteo Renzi, yana matsa lambar cewar ministan harkokin wajen kasarsa ta cancanci mukamin na kwamishinan harkokin wajen kungiyar, ko da shike ita kanta yanzu watanni hudu ke nan kawai ta yi kan wannan mukami a Italiya. A daura da haka, kasashen gabashin Turai, musamman shugaban Lithuania, Dalia Grybauskaite ta yi suka a game da karancin kwarewar Mogherini da kuma zargin kusancin da ke tsakaninta da Rasha. Wannan takaddama ta sanya shugabannin suka kasa yanke wasu kudirori kan karin kwamishinoni a sabuwar hukumar ta Kungiyar Hadin Kan Turai.
Daga cikin mukaman da ke bukatar mika su ga sabbin wakilai har da na shugaban majalisar shugabannin na Turai, wato wanda zai shugabanci majalisar shugabannin kasashe da na gwamatocin wannan kungiya. Dangane a haka, shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce:
"Wannan ba abu ne mai sauki ba, amma ni a imani na, wajibi ne a mayar da hankali ga zaben mutumin da yafi dacewa ya shugabancemu. Dangane da haka, ba zan mayar da hankali ga neman wani fifiko na siyasa ba, amma abin da yake da muhimmanci shi ne a zabi mafi dacewa da zai hademu wuri guda."
Burin al'amarin gaba daya shi ne ya zuwa watan Satumba a mikawa majalisar Turai sunayen manyan shugabanni da kwamishinonin hukumar ta Hadin Kan Turai, domin su yi muhawara kansu.
A taron na Bruessels, an bai wa sabon zababben shugaban hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai, Jean-Claude Juncker wa'adin zuwa karshen watan Agusta ya hada kwamishinoninsa 27 daga jerin kasashen wannan kungiya gaba daya. To sai dai masana suka ce ba su ga yadda Juncker zai sami nasarar yin haka ba, idan tun farko bai san wanda za'a bai wa mukamin kakakin kungiyar a harkokin waje ba, musamman saboda ganin cewar duk wanda aka zaba kan wannan mukami, kai tsaye shi ne mataimakin shugaban hukumar.
Duk da haka, shugabannin na Turai sun daidaita kan al'amuran ketare. A taron sun amince da fadada takunkumi kan Rasha. Nan gaba takunkumin zai shafi kamfanonin Rasha dake baiwa kungiyoyi masu goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine taimakon kudi, ko suke ba su taimako ta wasu hanyoyi daban. Kazalika, kamfanonin da ke taimakawa hukumomin Rasha da ke da hannu a ci gaba da ballewar gabashin Ukraine daga sauran kasar.
Karkashin takunkumin, an kuma umurci hukumar kungiyar hadin kan Turai ta dakatar da aiyukan taimako raya kasa a Rasha, ko da shike 'yan diplomasiya na kungiyar suka ce ba burinta ba ne ta gurgunta tsarin tattalin arziki ko hana Rasha ciniki gaba daya.
Mawallafi: Bernd Riegert/Umaru Aliyu
Edita: Suleiman Babayo