Firaiministan Isra'ila ya ziyarci Masar
September 13, 2021Talla
Shugaba al-Sisi ya karbi bakuncin Bennett a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh, sun kuma tattauna kokarin farfado da shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Faladsinawa.
Masar, kasa mafi yawan al'umma a kasashen Larabawa, ta zama ta farko da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila a shekarar 1979, bayan shekaru da dama na kiyayya.
A cikin watan Mayu, gwamnatin Alkahira ta taka muhimmiyar rawa wajen kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas da ke mulkin zirin Gaza, bayan shafe kwanaki 11 ana gwabza kazamin fada.