Shugabannin Turai sun Jaddada hadin kan EU
March 25, 2017Yarjejeniya ta farko da aka rattaba wa hannu tsakanin shugabannin kasashe na wancan lokaci, ita ce ta bada damar kafa kungiyar Tarayyar Turai. Shugabanni 27, tare da shugabannin manyan ma'aikatu na Tarayyar, sun jaddada sa hannunsu kan yarjejeniyar ta birnin Rome a cikin zauren da shekaru 60 baya, aka rattaba hannun a cikinsa a ranar 25 ga watan Maris na 1957.
Sakataren zartaswa na Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker, ya sa hannu a kan yarjejeniya da wani alkalami na asali, irin wanda a wancan lokaci shugaban kasar Luxembourg ya rattaba hannu da shi a cewar Mista Juncker.
"Kwarai kuwa abokaina, ya kyautu mu kara farin ciki dangane da Tarayyar Turai, domin mun samar da zaman lafiya mai dorewa a nahiyar baki daya. Sannan mun yi nasarar samar da kudi na bai daya a wannan nahiya."
Kafin a sake jaddada saka hannu kan yarjejeniyar, sai da Shugaban hukumar hadin kan Tarayyar Turai Donad Tusk ya yi kira ga shugabannin 27 da su nuna cewa sune shugabannin Turai, ta hanyar cikaken hadin kai.