1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shugabar EU von der Leyen ta samu karin wa'adi na biyu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 25, 2024

EU din ta amince da tsohon firaministan Portugal Antonio Costa a matsayin shugaban majalisar dokokinta

https://p.dw.com/p/4hU55
Hoto: Denis Balibouse/KEYSTONE/REUTERS/dpa/picture alliance

Jagororin kungiyar tarayyar Turai EU sun amince da sake bai wa shugabar kungiyar Ursula von der Leyen wa'adi na biyu, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA.

Karin bayani:Kasashen Turai na shirin zaben shugaban EU

Haka zalika jagororin kungiyar sun amince da tsohon firaministan Portugal Antonio Costa a matsayin shugaban majalisar dokokin tarayyar Turan na gaba.

Karin bayani:Von der Leyen za ta nemi shugabancin EU a wa'adi na biyu

Shi kuwa firaministan Estonia Kaja Kallas, shi aka zaba a mukamin babban jami'in diflomasiyyar kungiyar.

Wannan ci gaba na zuwa ne gabanin babban taron kungiyar da za a gudanar a ranakun Alhamis da kuma Juma'a a birnin Brussels, don sanar da sabbin shugabanninta da za su jagorance ta nan da shekaru 5 masu zuwa.