Gwamnatin Jamus ta amince da koran mai-gabatar da kara
August 5, 2015Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta goyi bayan ministan shari'a bisa matakin koran babban mai-gabatar da kara na gwamnati. Tuni matakin ya fito da irin sabanin da ake da shi kan 'yancin aikin jarida da kuma kare sirrin gwamnati. Mai magana da yawun gwamnati ta ce bisa wannan mataki shugabar gwamnatin ba ta da ja.
A wannan Talata da ta gabata ministan shari'a Heiko Maas ya bayyana fitar da Harald Range mai gabatar da kara na gwamnati daga bakin aiki, bayan da mai gabatar da karan ya zargi ma'aikatar shari'a da cewa ta saka baki kan aikin da yake yi, inda aka bukace shi da ya yi watsi da bincike da ake yi kan wasu 'yan jarida biyu.