1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar Gwamnatin Jamus ta soki matakin shugaba Trump

Salissou Boukari
January 29, 2017

Kasashe da dama na ci gaba da sukar matakin da shugaban Amirka ya dauka na hana 'yan wasu kasashen shiga kasar. Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce matakin ba mai gamsarwa ba ne.

https://p.dw.com/p/2Wamu
Deutschland Bundeskanzlerin Angela Merkel
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/H. Knosowski

Ta bakin kakakinta Steffen Seibert, Merkel ta ce wannan mataki na shugaba Trump ba abu ne mai gamsarwa ba. Inda ta ce ta yi imanin ko a cikin tsari na yaki da ta'addanci, bai halasta a saka mutane gaba daya cikin zargi ba, ta dalilin inda suka fito ko kuma adinansu ba.

Wasu 'yan majalisar dokokin Amirka Judy Chu, da kuma Nanette Barragan, sun isa a filin jirgin sama na Los Angeles domin samun cikeken bayani ga jami'an tsaro, don sanin kan abubuwan da ke gudana inda ta ce: "Mu yanzu abun da muke jira a nan shi ne na samun bayannai kan halin da mutanen ke ciki, amma kuma sun ki bamu bayannan kai tsaye. Kuma mu muna nan muna bukatar wadan nan bayannai."