1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala zaben shugaban kasar Taiwan

Abdul-raheem Hassan
January 11, 2020

Akalla akwai tazarar kuri'u sama da miliyan guda tsakanin 'yan takarar biyu da suka fafata a zaben neman shugabancin kasar, inda shugaba Tsai Ing-wen ke da rinjaye zuwa yanzu.

https://p.dw.com/p/3W2vE
Taiwan Präsidentschaftswahl 2020 | Tsai Ing-wen
Hoto: imago images/ZUMA Press/C. L. Hei

An kammala kada kuri'un zaben shugaban kasar Tailan lami lafiya, sai dai alamu na nuna cewa Shugaba Tsai Ing-wen za ta samu damar yin mulki wa'adi na biyu saboda yi wa abokin karawarta Han Kuo-yu zarra da yawan kuri'u.

Shugaba Tsai ta jam'iyyar DPP ta dare karagar mulki a shekarar 2016, kuma ana ganin wannan zabe zai taka rawa sosai na raba gari tsakanin Taiwan da gwamnatin China mai ikirarin tsibirin na karkashin ikonta.