Siriya: Aikin masu bincike a Douma ya fuskanci cikas
April 18, 2018
A daidai lokacin da tawagar kwararrun binciken makamai masu guba ta Majalisar Dinkin Duniya ke samun tsekon shiga a unguwar Douma don tattara bayanai kan zargin amfani da iska mai gubar da ta halaka gwamman mutane, makwonni biyun da suka gabata, ana ci gaba da samun cece-kuce kan zargin Rasha da da lalata shaidar amfani da iska mai guba a yankin.
A yanzu haka,tawagar binciken dai na nan na jiran samun tabbacin cikakken tsaro daga dakarun Siriya da na Rasha don sake shiga unguwar ta Douma, bayan da a jiya ta fice wurjanjan, sakamakon bude wa tawagar tsaronta da ta fara shiga yankin wuta. To sai dai wakilin kasar ta Siriya a zauren Majalisar Dinkin Duniya, Basharil Ja,afari ya musunta wannan batu:
“Isar tawagar birnin Damascus ke da wuya ta fara gudanar da aikin tattara bayanai da gwaje-gwajen wadanda ake cewa sun shaki gubar. Batun shiga unguwar Douma batu ne da ya rage wa tawagar tsaron, babu wanda ya hanata shiga. Jita-jita kawai ake yadawa don sanya shakku a sakamakon aikin tawagar binciken, don kuma a yi rufa-rufa ga hare-haren cin zalin da aka kai mana.”
To sai dai kamar yadda Andrew Tharos, kakakin tawagar binciken ke tabbatarwa, gwaje-gwajen wadanda ake zargin sun shaki gubar kadai ba zai wadatarba:
“Za mu yi kokarin tattara sinadaran da baragujen da ke yankin da bama-baman suka fashe. Aiki ne da ke bukatar tsaro da nutsuwa da za mu yi shi cikin yankin na Douma. Muna bukatar tantance sanadarin da ke unguwar da wanda za mu iya samu daga wadanda ake cewa harin ya ritsa da su.”
Tuni ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya nuna al,ajabinsa da yadda Majalisar Dinkin Duniyar ta biye abin da ya kira wasan kwaikwayon da ba shi da tushe ballantana makama:
“A gaskiya 'yar amuntan da ke tsakaninmu da abokanmu na kasashen Yamma ta gama sukurkucewa, musammama bayan hare-harensu kan Siriya tun kafin gudanar da bincike. Ban ga dalilin tura wannan tawagar ba, bayan sun kai wa Siriya hare-harensu na cin zali, kan banda kokarin halatta wadannan hare- haren. Domin bincikenmu ya tabbatar mana da cewa, babu wani makami mai guban da aka yi amfani da shi kan unguwar Douma.”
Tun kafin fara aikin tawagar dai, dama kasashe ukun da suka yi gaban kansu wajen kai wa Siriyan hare-haren da suka ce na ramuwar gayya ne, wato Amirka da Faransa da Birtaniya, suke ta zargi Rasha da bad da sawun shedun da za su iya kaiwa ga tabbatar da zargin yin amfani da guba a yankin, batun da tawagar binciken ta ce, bincikenta ne kadai zai rabe ma ta zare da abawa.
A hanu guda, a wani abun dake nuna alamar neman sake maid a kasar ta Siriya sabon filin daga, adaidai lokacin da ake ganin kamar rikicin kasar yazo karshe, kasar Saudiya, tace tana daf da cimma yarjejeniya da Amirka da za ta ba ta dammar girke sojinta a Siriya,don yin aiki tare da kawancen Amirka, lamarin da ko shakka babu, zai iya kaiwa ga gwabzawar gaba da gaba tsakaninta da babbar abokiyar hamayyarta Iran a cikin kasar ta Siriya.