Farar hula na cigaba da tserewa daga yankin Idlib
January 17, 2020Talla
Bachelet ta kuma kara da yin Allah wadai da yadda bangarorin da ke rikici da juna a Siriya suke luguden wuta ta sama a yankunan da fararen hular ke zaune, a jiya Alhamis wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar daga watan Disambar bara zuwa yanzu akalla al'ummar Siriya da yawansu ya kusan dubu dari uku da hamsin, mafiya yawansu mata da kananan yara sun tsere daga yankin na Idlib zuwa makotan yankuna a iyakokin kasar da Turkiyya inda suke rayuwa cikin ragaita.