1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: An sako daruruwan firsinonin yaki

Yusuf Bala Nayaya
June 24, 2017

A cewar kamfanin dillancin labaran Siriya SANAA mafi yawa na fursinonin an sako su ne daga gidan kaso na birnin Damascus ciki kuwa har da mata 91.

https://p.dw.com/p/2fKVb
Syrien | Syrien atlässt zum Ende des Ramadan IS-Gefangene
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Gwamnatin Siriya a wannan rana ta Asabar ta saki fursinoni 672, ciki kuwa har da fursinonin siyasa ta yadda za su sami damar shiga a dama da su a shagulgulan Sallah karama.

A cewar kamfanin dillancin labaran Siriya SANAA mafi yawa na fursinonin an sako su ne daga gidan kaso na birnin Damascus ciki kuwa har da mata 91 kamar yadda ministan shari'a Hesham al-Shaar a kasar ta Siriya.

Bai dai yi karin bayani ba kan suwa aka saki da ma laifukan da suka aikata kafin a kai ga daure su. A cewar al-Shaar wannan wani mataki ne na shirin sulhu a matakin kasar ta Siriya da yaki ya daidaita. Um Rashed, daya ce daga cikin wadanda aka sako:

An tsare ni shekara guda saboda wasu rahotanni wadanda ba na gaskiya ba ne, mun gode wa Shugaba Assad saboda samu cikin shirin afuwar, da dama cikinmu sun fita saboda an gane bamu da laifi.

Tun dai da aka faro gangamin adawa da gwamnatin ta Siriya a watan Maris na 2011  dubban al'ummar kasar ne ake tsare da su baya ga dubban daruruwa da suka rasu da miliyoyin da suka kauracewa muhallansu.