Siriya: Ba a sake kai sabbin hare-hare ba
April 17, 2018Kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya na Sana ya ruwaito wata mijiyar sojin kasar ta Siriya na cewa a hakikanin gaskiya ba bu wani hari da kasar ta Siriya ta fuskanta daga waje a daren na jiya, illa dai kawai an tayar da jiniyar bindigogi masu kakkabo makamai masu linzami ne a bisa wasu bayanan kuskure da suka nunar da cewa kasar ta fuskanci wasu sabbin hare-haren makaman masu linzamin a daren na jiya.
A wannan Talata ce dai tawagar kwarraru na hukumar yaki da yaduwar makamai masu guba za ta isa a gabashin birnin Ghouta domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa sojojin Siriya na yin amfani da makami mai guba.
Wannan lamari dai ya wakana ne kwanaki uku bayan da kasashen Amirka faransa da Birtaniya suka kaddamar da wasu hare-haren makamai masu linzami kan wasu cibiyoyin sojin kasar ta Siriya a matsayin martani ga harin da ake zargin Siriyar ta kai da makami mai guba a kan 'yan tawaye na gabashin Ghouta.