EU ta kara wa'adin takunkumn Siriya
May 28, 2018Talla
Kungiyar ta EU ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Litinin inda ta ce ta dauki wadannan sabbin matakai ne ta la'akari da da yadda gwamnatin Siriyar ke ci gaba da kuntata wa al'umma fararan hula a kasar. Mutane 259 ne da suka hada da manyan jami'an gwamnati da kuma wasu manyan attajira na ciki da wajen kasar ta Siriya da ake zargi da tallafa wa gwamnatin Siriyar ne dai matakin ya shafa. Takunkumin da Kungiyar ta EU dai ta saka wa kasar ta Siriya ya tanadi haramta wa wadannan mutane shigowa kasashen Turai da kuma rike kudaden da suke ajiya a bankunan na Turai da ma kuma haramtawa kasar sayar da man fetur dinta a kasuwannin duniya.