1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: hare-hare kan 'yan tawaye

Ahmed SalisuMay 22, 2016

Jiragen yakin Rasha sun kai jerin hare-hare kan wani titi mai muhimmancin gaske da 'yan tawayen kasar da ke rikici da shugaba Bashar al-Assad ke rike da shi.

https://p.dw.com/p/1IsZs
Syrien Allepo Flugzeugangriff Ruinen
Hoto: Reuters

Kungiyar nan da ke sanya idanu kan kare hakkin bani Adama ta Syrian Observatory for Human Rights ta ce yawan farmakin dakarun Rashan sun kai akalla sun doshi 40.Wannan farmaki inji shaidun gani da ido shi ne mafi kamari da aka kai yankin da wannan titi na Castello ya ke tun bayan da aka cimma yarjejeniya tsagaita wuta a rikicin na Siriya.

Bayanan da ke fitowa daga inda aka kai wannan hari dai na cewar ba a kai ga jikkata kowa ba. Wannan titi na Castello dai na da muhimmancin gaske domin ta nan ne ake iya kaiwa ga wuraren da 'yan tawaye suka ja daga.