1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wani sabon hari a kasar Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afarJanuary 31, 2016

Wani mummunan hari da aka kai a kudancin Damascus babban birnin kasar Siriya ya hallaka a kallah sama da mutane 60 tare da raunata wasu sama da 100.

https://p.dw.com/p/1HmcR
Masallacin Sayyada Zainab da ya fuskanci harin ta'addanci a Siriya
Masallacin Sayyada Zainab da ya fuskanci harin ta'addanci a SiriyaHoto: Getty Images/AFP/L. Beshara

Wannan harin dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da bangarorin da ke yakar juna a Siriyan da kuma masu ruwa da tsaki ke halartar taro a birnin Geneva, domin kawo karshen rikicin kasar na tsahon shekaru wanda ya lakume rayukan dubun-dubatar 'yan kasar. Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya ta sanar da cewa harin da wasu 'yan kunar bakin wake biyu suka kai, an kai shi ne kusa da Masallacin Sayyida Zainab na Musulmi mabiya mazhabar Shi'a. A cewar Federica Mogherini shugabar sashen hulda da kasashen ketare ta kungiyar Tarayyar Turai EU, an kai harin ne domin dakile tattaunawar sulhun da ke gudana a yanzu haka a Geneva.