Siriya: Jama'a na cikin halin tsaka mai wuya a Idlib
MDD ta bayyana damuwa kan halin da ake ciki Idilib na Siriya inda yara da dama sun halaka a cikin yakin da ya tilasta wa dubunnan jama'a kaurace wa gidajensu daga birnin da ke zama tungar karshe ta 'yan tawaye.
Iyalai sun tsere saboda karuwar hare-hare
Sojojin Siriya sun zafafa hare-hare a muhimmin yankin da ke hannun 'yan tawaye a cewar Shugaba Bashar al-Assad. Yakin da ya haifar da gudun hijira zai iya zama mafi girma a karni na 21, a cewar shugaban hukumar agajin gaggawa ta MDD Mark Lowcock. Rikicin ya fi shafar yara kanana.
Hijira mafi girma tun yakin duniya na biyu
Kusan mutane 900,000 suka bar matsugunansu cikin watanni uku, kashi 80 mata ne da yara, in ji kakakin MDD. kusan mutane 300,000 suka yi hijira a farkon Febrairu kadai. Hijirar da ka iya zama mafi girma tun yakin duniya na biyu.
Yanayi mai kisa
Yanayin sanyi kasa da maki bakwai a ma'aunin celsius da dusar kankara da ta lullube sansanonin 'yan gudun hijira a kan iyaka da Turkiyya, ya halaka yara bakwai. Asusun kula da yara na MDD ya ce yara da iyaye na kona duk abin da suka samu dan dumama jiki. Akwai fargabar karuwar mutuwa.
Dakarun hadaka na Turkiyya
Tawagar motocin yakin Turkiyya ne ke dannawa tsohuwar tungarsu, yayin da sojojin Siriya da ke samun tallafin Rasha ke bude wuta domin sake kwace yankin a farkon watan Janairu. Bayan dakarun Turkiyya sun yada zango a wurin domin taimaka wa 'yan tawayen da aka kashe a farkon watan Febrairu, an yi yunkurin tsagaita bude wuta.
Tafiya ba masauki
Shugaba Assad ya dade da niyyar sake kwace babban titin da ya hada lardin Idlib da Aleppo, bayan Rasha ta taimaka wa sojojin Siriya kwace garuruwan da ke kusa da titin a ranar 11 ga watan Febrairu, barin wuta a Aleppo ya tilasta sama da mutane 43,000 hijira zuwa iyakar Turkiyya.
Rasha na ta da bamabamai na kan mai uwa da wabi
Harin sama da sojojin Rasha da Siriya suka yi kan sansanonin gudun hijira da asibitoci da makarantu ba na rashin sani ba ne, in ji kakakin hukumar kare hakkin dan Adam a MDD Rupert Colville, ya ce fararen hula 299 suka mutu a 2020, kashi 93 sun mutu sanadin hare-haren dakarun gwamnati da kawayenta. Shugaban hukumar kare hakkin bil Adam ta MDD Michelle Bachelet ya kira matakin da ganganci.
Martanin 'yan tawaye da mayakan jihadi
'Yan tawayen da Turkiyya ke mara wa baya sun yi barna, kamar mayakan jihadi da ba sa samun goyon bayan gwamnatin Ankara a hukumance. Kungiyar Hayat Tahrir al-Sham, ta kakkabo jirgin yakin sojojin Siriya da ke jefa bama-bamai kan fararen hula.
Neman tsira
MDD ta ce ba matsugunin da ke da kariya kuma masu gudun yaki sun cika sansanonin 'yan gudun hijira. Yawanci sun bar sansanonin domin gwada sa'arsu a kan titi. Kwamishinan kula da hakkin dan Adam na MDD Bachelet ya bukaci ba wa fararen hula damar tsira da rayuwarsu.
Ba sauran mafita
Turkiyya ta rufe iyakarta domin hana kwararar 'yan Siriya. Yanzu haka tana tsugunar da 'yan gudun hijira miliyan uku da rabi. Matakin da ya bar mazauna Idlib ba hanyar tsira. Sama da mutane 500,000 da suka yi hijira kananan yara ne.