Siriya: Kasashen Larabawa sun gana da al-Assad
February 26, 2023Tawagar dai ta hada da wakilan kasashen Jordan da Falasdini da Libiya da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman da kuma Lebanon. A cewar dan majalisar dokokin Iraqi Mohammed Halbousi ya ce, tsakaninsu da kasar Siriya tamkar dan juma ne da dan jumai domin haka suke fatan alaka ta sake karfafa a tsakaninsu. Dangantaka dai ta fara inganta tsakanin kasar da sauran takwarorinta ne tun bayan da ta fuskanci mummunar girgizar kasar a farkon wannan watan na Fabarairu wanda ya halaka mutane kimanin dubu 6 a Siriyar.
Kasar Siriya dai ta kasance mujiya a cikin tsintsaye a tsakanin kasashen Larabawa tun bayan da shugaba al-Assad ya murkushe masu zanga-zanagar adawa da gwamnatinsa a shekarar 2011. A shekarar ce kuma kungiyar kasashen Larabawa ta dakatar da kasar Siriya daga zama mamba a cikinta, yayin da kasashe da dama suka janye jakadunsu daga birnin Damascus.