1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Kokarin samun mafita kafin sumame a Idleb

Salissou Boukari
August 31, 2018

Ana ci gaba da tattaunawar neman mafita tun 'yan kwanaki, domin kauce wa afka wa yankin Idleb da sojojin gwamnatin kasar Siriya masu samun goyon bayan Rasha ke shirin yi.

https://p.dw.com/p/344su
Syrien Idlib Provinz - Türkischer Convoy
Hoto: Getty Images/AFP/O. H. Kadour

Kimanin kashi 60 cikin 100 na yankin na Idleb na a hannun 'yan jihadi na kungiyar Hayat Tahrir al-Cham, tsohuwar kungiyar Al-Qaïda a kasar ta Siriya, da kuma wasu gungu biyu na 'yan tawaye. Tun dai yau da 'yan kwanaki ne sojojin na Siriya suka ja daga, inda suke shirin afka wa yankin na Idleb, wanda kungiyoyin agaji na kasa da kasa da ma Turkiyya ke neman kauce wa yin hakan da suka ce zai haddasa babbar matsala ta kwararar 'yan gudun hijira da ma kashe-kashen fararen hulla.

A halin yanzu dai ana tattaunawa ta koli a tsakanin kungiyoyin da Turkiyya, wanda muddin ba a cimma matsaya ba, babu makawa Sojin na Siriya masu samun goyon bayan Rasha, Iran da ma Hezbollah na Lebanon za su kai wannan sumame.