Siriya: Mutane da dama sun mutu a wani harin roka
March 21, 2018Talla
Kamfanin dillancin labaran kasar na Sana ya ruwaito cewa akasarin mutanen da suka mutu a cikin harin wanda aka kai kasuwar da ke kusa da wani shingen bincike na sojojin kasar, fararan hula ne. Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa harin ya ritsa da yara kanana da dama.
Wannan hari ya zo ne lokacin da sojojin gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad masu samun goyon bayan kasar Rasha ke ci gaba da lugudan wuta a birnin Goutha da ke zama tungar karshe ta 'yan tawayen kasar ta Siriya inda fararan hula sama da dubu daya da 450 suka halaka a wata daya na wannan farmaki.