1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya na ci gaba da luguden wuta a Ghouta

Mouhamadou Awal Balarabe
March 11, 2018

Mutane 1031 sun rasa rayukansu ciki har da yara kanana 219 tun bayan da sojojin da ke biyeyya ga shugaba Bashar al-Assad na Siriya suka fara barin wuta a yankin Ghouta kwanaki 20 ke nan da suka gabata.

https://p.dw.com/p/2u6qR
Syrien Blutvergießen in Syrien geht weiter - Hilfsorganisationen können Ost-Ghuta nicht erreichen
Hoto: Reuters/B. Khabieh

Sojojin gwamnatin Siriya na ci gaba da kai farmaki kan 'yan tawaye a gabashin Ghouta, bayan da suka yi wa birnin Duma da ya kunshi dimbin masu tada kayar baya kawanya. Gamayyar Kungiyoyin kare hakkin bil Adama ta kasar ta bayyana cewar fararen hula 1031 ne suka rasa rayukansu ciki har da yara 219 tun bayan da sojojin da ke biyeyya ga shugaba Bashar al-Assad suka fara barin wuta a wannan yanki kwanaki 20 ke nan da suka gabata. Sannan an kiyasta cewar mutane 4350 sun ji rauni.

A cewar tashar talabijin din Syria, rundunar sojojin kasar ta ninka hare-haren da take kaiwa a yankuna da dama na kasar, inda ta yada shiri kai tsaye kan halin da daruruwan fararen hula ke ciki a birnin Misraba. Kudirin tsagaita bude da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi bai sa gwamnatin Siriya dakatar da bude wuta a gabashin Ghouta ba, lamarin da ya sa kungiyoyin agaji nuna fargaba kan halin da fararen hula ke ciki. Ayarin biyu na kayan abinci da magunguna ne kawai aka yi nasarar shigarwa gabashin Ghouta tun 18 ga watan jiya lokacin da sabon rikicin ya barke.