Siriya: Putin ya tattauna da Macron
February 9, 2018Tattaunawar ta shafi batun shirin ziyarar da shugaban na Faransa zai kai zuwa Rasha, inda zai halarci babban zaman taro kan tattalin arziki da zai guda a birnin Saint-Pétersburg na kasar ta Rasha daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Mayu a cewar fadar shugaban kasar ta Rasha ta Kremlin cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din.
Bangarorin biyu na Rasha da Faransa sun sanar da bukatunsu na ganin an ci gaba da tattaunawar da ake ta neman sulhu a rikicin Siriya, inda suke ganin ya kyautu a karfafa hulda tsakanin kasashen biyu wajen walwale wannan rikici. Daga bisani shugabannin biyu sun kuma tattauna batun kasar Ukraine, inda suka nuna mahimmancin aiwatar da yarjejeniyar nan ta zaman lafiya da aka cimma ta birnin Minsk da ke da burin kawo karshen rikicin gabashin kasar Ukraine.