1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai hari Siriya

November 6, 2022

Shaidun gani da ido a Siriya sun ce, wani jirgin yakin Rasha ya kai hari kan wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da yankin arewa maso yammacin Idlib.

https://p.dw.com/p/4J89q
Syrien Flüchtlingscamp Idlib Bombardierung
Hoto: Izzeddin Kasim/AA/picture alliance

A cewar kungiyar kare hakkin bil'Adama ta Siriya da ke da mazauni a Birtaniya, dakarun sun harba kimanin rokoki 30 ne kan sansanin na Maram, inda kimanin fararen hula tara suka rasa rayukansu yayin da wasu gommai suka jikkata.

Rahotannin sun yi nuni da cewa daga cikin wadanda suka gamu da ajalin nasu ciki har da yara uku da kuma mace daya.

Kawo yanzu dai Rasha ko ma kawancen dakarun Siriya ba su bayar da karin bayani kan harin da suka ce, sun kai ne ga maboyar 'yan ta'adda tare da musanta zargin kai harin kan fararen hula.

Alkalumma na nuni da cewa, kimanin mutane miliyan 4 ne ke rayuwa a yankin mai yawan jama'a da ke kusa da iyakar kasar da Turkiyya.