Siriya: Kwashe 'yan tawaye daga Aleppo
December 15, 2016Talla
Shaidun gani da ido sun ce an ga fararan motocin daukan marasa lafiya, da kuma motocin bas-bas masu launin tsanwa da tsakiyar ranar Alhamis na ta shiga yankunan da 'yan tawaye suke domin fitar da su, musamman ma wadanda suka samu raunuka da iyalansu. Tuni dai kungiyar agaji ta Red Cross da ke kasar ta Siriya ta tabbatar da hakan, inda ta ce tuni mutane suna ta shiga cikin motocin, kuma motocin za su yi ta zuwa da zowa.
A cewar gidan telebijin din kasar ta Siriya, wannan aiki ya shafi akalla 'yan tawaye 4000 da iyallansu. Tun dai a shekara ta 2012 ne 'yan tawayen na Siriya suka kwace birnin na Aleppo da ke a matsayin birni na biyu mafi girma a kasar, kuma kwace shi a halin yanzu ba karamin koma baya ne ga 'yan tawayen ba.